20 Afirilu 2021 - 14:55
Sojojin Kasar Chadi Sun Sanar Da Rusa Rundunar ‘Yan Tawaye

Tashar talabijin din gwamnatin kasar ta Chadi ta nuna sojoji sun a murnar samun galaba akan ‘yan tawaye a kusa da konannun motoci da kuma mayakan da aka kama a matsayin fursunoni.

ABNA24 : Sanarwar ta kunshi cewa an kashe ‘yan tawayen da su ka kai 300 a fadan da aka yi a yankin Kanem ta Arewa, sai kuma wasu 150 da aka kama a matsayin fursunoni.

Kakakin sojan kasar ta Chadi Azem Bermandoa Agouna ya ce; An rusa ilahirin rundunar ta ‘yan tawaye.

A ranar 11 ga watan nan na Aprilu ne dai kungiyar ‘yan tawayen kasar ta Chadi wacce take kiran kanta; Rundunar kawo sauyi’ da kuma take da matsuguni a yankin kan iyaka da kasar Libya, ta kai wani hari akan cibiyoyin zaben kasar,a daidai lokacin da ake zaben shugaban kasa.

Kungiyar ta riya cewa ta ‘yantar da yankin Kanem daga karkashin ikon gwmanatin N’Djamina, sai dai gwamnatin ta Chadi ta karyata zargin.

342/